Daga Shu’aibu Ibrahim Gusau
Jagoran lauyoyin Jam’iyyar APC a Jihar Zamfara, DC Enwelum ya bayyana cewa, sun sha alwashin yin duk mai yiyuwa a hukuman ce domin ceto Jam’ iyyar da ‘ya’yan ta daga abin da suka kira cin amanar da ake neman jefa su a ciki, sanadiyar canza sheƙar da Gwamnan Jihar, Bello Mohammed Matawallen Maradun .
Hakan yana kunshe ne cikin wata takarda mai dauke da da hannun Shugaban Kwamitin Yaɗa Labarai na Kwamitin Riƙon Kwaryar Jam’iyyar APC na Jihar Zamfara, bangaren tsohon gwamnan jihar zamfara, Hon Ibrahim Muhammad Danmadami.
Da yake Jagorantar ayarin Lauyoyi 4 wajen shigar da ƙarar a gaban babbar Kotun Tarayya dake Gusau, Babban Birnin Jihar Zamfara ranar Litinin 12/7/2021, mai magana da yawun bakin su, DC Enwelum SAN ya ce sun garzayo zuwa Kotun ne domin neman ta yi masu fashin baƙin wasu lamurran da suka ɗaure masu kai, musamman batun rusa shugabancin halattacen Kwamitin riƙon ƙwarya na Jam’iyyar APC, tun daga matakin Jiha zuwa matakin Mazaɓun dake faɗin Jihar ta Zamfara.
DC Enwelum SAN wanda shine yake jagorantar gungun lauyoyin da suke kare masu shigar da ƙarar, ya ce sam baza ta saɓu ba, su zura ido suna kallon ana yi ma tsarin mulkin Jam’iyyar Karan tsaye, domin biyan buƙatar wani mutum ko wasu mutane.
KARANTA WANNAN LABARIN: Sojin ruwa ta karyata wani rahoton kan dauka sabbin jami’an
Ya ce babu hujja idan aka yi la’akari da tanade – tanaden sassa daban daban na Kundin tsarin mulkin Jam’iyya musamman sashe na 13.3 (III), da sashe na 14.I (III), (VI), (VIII) da kuma sashe na 17.I, babu wata halattacciyar hujja ko hujjojin da Shugaban Kwamitin Riƙon Ƙwarya na Jam’iyyar a matakin Ƙasa kuma Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni yayi amfani da su wajen aiwatar da wannan aika – aikar da ke iya kawo ma Jam’iyyar cikas a Jihar Zamfara.
Ya ce ‘yayan Jam’iyyar APCn Jihar Zamfara sun kaɗu sosai da wannan furuci na Gwamna Mai Mala Buni, saboda haka ne suke neman Kotun da ta taka ma Kwamitin shi burki, tare da hana Hukumar Zaɓe mai cin gashin kanta ta Ƙasa amincewa da waɗan nan Sabbin Shugabannin Jam’iyyar na Jiha da aka ayyana.
Mr. DC Enwelum SAN, ya nemi ‘yayan Jam’iyyar APC na Jihar Zamfara da su kwantar da hankalin su, su kuma ci gaba da zama tsintsiya maɗaurin ki ɗaya, domin su kam sai sun ga abin da ya kwance ma Buzu nadi a wannan Shari’ar In Shaa Allah.
Comments 2