Jami’iyar adawa ta PDP reshen Jihar Kano, ta yi Fatali da bukatar yin Murabus din Shugaban jam’iyar na Kasa Prince Uche Seconds daga mukamin shi.
Shugaban jam’iyar a jihar Alhaji Shehu Sagagi ne, ya yi Fatali da bukatar yin Murabus din Shugaban jam’iyar ta Kasa, lokacin da ya ke zanta wa da manema labarai a garin Kano a jiya Laraba.
Sagagi ya ce, ” Muna goyan bayan Shugaban jam’iyar PDP na Kasa, sabida bai yi wani abu wanda ba dai-dai ba, da har za’a bukaci ya yi murabus daga mukamin shi”. Inji shi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan sanda sun Garkame Ofishin jam’iyar APC a Enugu
Ya kuma kara bayyana cewa, jam’iyar na da masaniya kan wasu mabobin ta, da ke aiki tare da na jam’iyar APC Mai mulki, domin haifar da rikicin cikin gida a dukkannin matakai na Jam’iyar PDP, bisa kudirin su na ganin kawo rashin dai-dai-to a jam’iyar, domin hana ta karbar Mulkin kasar nan, a babban zaben shekarar 2023 mai zuwa.
A wani labarin Kuma.
Matsalar Tsaro: Gwamnatin Kaduna ta bukaci Karin Soji
Gwamnatin jihar Kaduna ta bukaci hukumomin tsaron Soji, da su kara zuba jami’an su a jihar, domin magance hare-hare Yan bindiga da kuma Garkuwa da mutane.
Mataimakiyar Gwamnan jihar Dakta Hadiza Balarabe ce, ta yi wannan rokon lokacin da take tarban Babban Hafsan sojin kasar nan Laftanar Janar Faruk Yahaya, da kuma wasu manyan jami’an sojin a dakin taro na Sir Kashin Ibrahim House da ke Kaduna, a jiya Laraba.
Mataimakiyar Gwamnan ta ce, ” Karin jami’an tsaro a jihar zai taimaka wajan magance hare-hare yan bindiga da kuma satar mutane a fadin jihar” inji ta.
Balarabe ta ce, Karin jami’an tsaro da aka samu a cikin garin Kaduna ya haifar da da Mai Ido, amma kuma ta bukaci Babban Hafsan sojin da ya karo wasu jami’an, domin shafe yan bindiga daga doran kasa.
Mataimakiyar Gwamnan ta kuma bukaci Karin jami’an soji a garin Rigachikun dake karamar hukumar Igabi na jihar, inda ta ce, kafa sansanin soji a yankin da a ka Kai hari a kwana-kwanan nan, zai taimaka gaya wurin magance matsalar tsaro.
Ta kuma kara da cewa, ya kamata rundunar sojin ta duba yuwuwar kara jami’an ta a yankin Kudancin Kaduna baki daya, musamman ma a garin Zangon-Kataf, sabida rikice-rikicen da ake samu a yankin.