Gwamna Darius Ishāku na jihar Taraba ya lashe zaben fidda gwani na jam’iyyar PDP a kudancin Taraba.
Ya samu kuri’u 154 wadda ya lashe zaben fidda gwanin.
An gudanar da zaben fidda gwani cikin lumana amma karkashin tsauraran matakan tsaro a Wukari.
Mataimakinsa Ishāku, Alhaji Haruna Manu, shi ma ya lashe zaben fidda gwani na sanatan Taraba ta tsakiya.
Haruna ya samu kuri’u 143 inda ya doke Muhammed Abana wanda bai samu kuri’u ba. An gudanar da zaben fidda gwani na shiyyar Taraba ta tsakiya a Bali.
Sanata mai wakiltar Taraba ta Arewa a majalisar dattawa, Alhaji Shuaibu Isa Lau shi ma ya lashe zaben fidda gwani da aka gudanar a filin wasa na Jolly Nyame da ke Jalingo.
Sanata Lau ya samu kuri’u 193 inda ya doke sauran ‘yan takara uku.
Yan takara uku da Lau ya kayar da su sun hada da David Kassa wanda ya samu kuri’u 73 da Mista Jeji Williams da ya samu kuri’u 5 da kuma Mista Bandawa wanda bai samu ko da kuri’a daya ba.
A wani labarin Kuma na daban.
Yan bindiga Sun Baiwa Gwamanati Awa 48, Ta Yi Gaggawan Janye Sojoji Daga Yankin Kudu Maaso Gabas
Wadanda ake zargin sun kashe dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Aguata II a majalisar dokokin jihar Anambra, Okechukwu Okoye, sun bai wa masu rike da mukaman siyasa umarnin gaggawar janye sojoji daga yankin Kudu maso Gabas cikin sa’o’i 48 masu zuwa.
Wannan wa’adin yana kunshe ne a cikin wata wasika da aka samu a gefen shugaban ya kin Dan Majalissar da aka kashen.
Okoye, wanda aka yi garkuwa da shi tare da mai taimaka masa, Cyril Chiegboka, har zuwa yanzu ba a tantance wadanda suka kai harin ba a ranar 15 ga Mayu, shekarar 2022, daga bisani masu garkuwa da mutane suka sare masa kai, tare da na mataimakinsa, a kan hanya a Amichi, a ranar Asabar, inda Kuma suka yi garkuwa da su a kwanakin baya. Tare da rubutacciyar wasika
Duk da cewa ruwan sama da aka yi a wannan rana ya wanke wasu daga cikin kalmomin.
Mummunan kisan gillar da aka yi wa dan majalisar da mai taimaka masa ya haifar da fargaba da martani daga masu ruwa da tsaki a jihar.
Sai dai kwamishinan ‘yan sandan jihar, Echeng Echeng, yayin da yake kirashi domin samun cikakken bayani daga al’ummomi daban-daban domin bankado ‘yan bindigar, ya yi watsi da wannan barazanar, yana mai cewa ba “an san su ba” amma “an san su”.
Ya kuma sha alwashin gurfanar da masu aikata laifuka a jihar a gaban kotu.