Kwamitin gudanarwa na jam’iyar PDP reshen jihar Edo, ya janye dakatarwar ya yi wa Shugaban Jam’iyar jihar Dakta Tony Aziegbemi.
Sakatare yada labarai na jam’iyar PDP reshen jihar Chris Nehikhare ne ya bayyana hakan, a yau Asabar, a Benin babban birnin jihar.
Nehikhare ya ce, ” Mun dauki wannan matakin ne bayan mambobin jam’iyar a jihar, sun karbi rahoton da Kwamitin da aka nada, domin gudanar da binciken a kan zargin rashin da’a, da ake wa Shugaban jam’iyar Honarabul Tony Aziegbemi, inda rahoton ya wanke shi, kuma hakan yasa mu ka janye dakatarwar ” inji shi.
Kazalika hakan ya tabbatar dace wa, Shugaban jam’iyar PDP reshen jihar zai dawo bakin aikin shi nan ta ke.
KARANTA WANNAN LABARIN: Harsashi ya kashe wata a zanga-zangar Legasa
A karshe ya ce “Mun yaba wa dukkannin mambobi, da magoya bayan jam’iyar, da kuma jagorori jam’iyar, biyo bayan irin hadin kai da kuma cikakken goyan baya da su ka bada, a lokacin gudanar da wannan bincike” inji shi.