Kwamitin Gudanarwa na jam’iyyar PDP na kasa ya dage babban taron jam’iyar shiyar Arewa maso Yamma, wanda tun farko aka shirya gudanarwa a ranar 20 ga watan Nuwamba.
Jam’iyyar a cikin wata sanarwa da sakataren kungiyar ta kasa, Kanal Austin Akobundu (mai ritaya) ya fitar a ranar Laraba a Abuja, ta ce NWC ta amince da dage taron ne bayan tuntubar juna.
“An yanke shawarar ne a kan wasu yanayi da ba’a yi tsammani ba, da za su iya yin tasiri sosai ga gudanar da taron.”
“kwamitin Zartaswa NWC tana kira ga duk masu ruwa da tsaki, shugabanni da mambobin jam’iyyarmu a yankin Arewa maso Yamma da kuma a fadin kasar nan da su lura da cewa za a sanar da sabbon ranar da za’a gudanar da Taron a kan kari,” in ji Akobundu.
Comments 1