An Bayyana Mista Ibrahim Gajere na Jam’iyyar adawa ta PDP a matsayin wanda ya lashe zaben Shugaban Karamar Hukumar Kajuru, na jihar Kaduna.
Jami’in hukumar Zaben jihar a yankin Dr Ibrahim Dan Maraya na jami’ar jihar ne ya sanar da sakamakon zaben a safiyar Yau Lahadi.
Dan Maraya ya ce, Ibrahim Gajere na jam’iyar PDP ya samu kuri’u 14,432, inda ya kayar da dan takarar jam’iyyar APC, Cafra Caino, wanda ya samu kuri’u 9,095.
Idan za’a iya tunawa dai, Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Kaduna KAD-SIECOM, da farko ta sanar da ranar 4 ga Satumba don gudanar da zaben.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gaskiyar Lamari kan Jita-Jitan Auren Amaryar Kamaye
Inda daga bisani hukumar ta dage zaben zuwa ranar Asabar 25 ga watan Satumba shekarar nan, saboda dalilan tsaro.
A wani labarin Kuma na daban.
Kungiyar likitocin masu neman kwarewa ta Najeriya NARD a ranar Asabar ta baiwa Gwamnatin Tarayya wa’adin sa’oi 72 don biyan bashin albashin membobinta a dandalin GIFMIS, da na Asusun Horar da Ma’aikatan Lafiya MRTF.
Ta bayyana cewa yajin aikin da aka fara a ranar 2 ga watan Agusta, 2021, don kawo karshensa, akwai bukatar gwamnati ta biya mafi karancin bukatunta, wanda kuma ya hada da biyan albashin watan Agusta da Satumba da aka hana,na janye karar da aka shigar a gaban kotu, biyan albashi da alawus alawus da ake bin membobinta a cibiyoyin kiwon lafiya na manyan makarantu na jihar, da sauran su.
Shugaban kungiyar NARD, Dakta Dare Ishaya ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa a karshen Babban Taron Kungiyar na Shekaru 41 AGM na Taron Kimiyya a Bauchi.
Yace“AGM ya zargi gwamnatin tarayya da kai NARD kotu saboda yajin aikin da ake yi don neman inganta rayuwar membobin mu.” Sun yi tir da mambobin dake cikin mawuyacin hali a dandalin GIFMIS da suke fuskantar saboda jinkirin biyan albashinsu daga watanni uku zuwa takwas.
AGM ta buƙaci gwamnatin tarayya da ta tabbatar da waɗannan abubuwan cikin gaggawa don manufar dawo da yanayin al’ada ga sashin kiwon lafiya, Biyan Horar da Likitoci masu neman kwarewa a cikin awanni 72, tunda kuɗin da akayi nufin yana samuwa da tabbatar da jerin sunayen don biyan kuɗi an kammala, Biyan basussukan albashin membobin mu akan dandalin GIFMIS a cikin awanni 72 yayin da ake ci gaba da yin ƙaura, Da janye karar da aka shigar damu a gaban kotu don a samu zaman lafiya, Biyan albashin da aka hana a watan Agusta da Satumba.
Yakamata gwamnatin tarayya tayi nasara akan gwamnatocin jihohi daban daban da su gaggauta biyan basussukan albashi da alawus alawus da ake bin membobin mu a cibiyoyin kiwon lafiya na manyan makarantu na jihar kamar yadda aka bayyana a sama.
Comments 1