Francis Zimbo na jam’iyyar Adawa ta PDP, ya lashe zaben shugaban karamar hukumar Zango Kataf na jihar Kaduna.
Kamfanin Dillancin Labaran Kasar Nan NAN ya ruwito cewa, Tun da fari an dage zaben ne zuwa jiya Asabar, saboda matsalar tsaro da yankin ke fama da shi.
Da yake bayyana sakamakon zaben a yau Lahadin jami’in zaben Nuhu Garba ya ce, Mista Zimbo ya samu kuri’u 28,771 inda ya kayar da John Hassan na jam’iyyar APC Mai mulki, wanda ya samu kuri’u 19,509, a zaben da ya gudanar.
“Mista Francis Zimbo na jam’iyyar PDP, bayan ya cika ka’idojin doka kuma ya sami mafi yawan kuri’un, an tabbatar da shi a matsayin wanda ya lashe zaben,” in ji Farfesa Garba.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan bindiga sun Farmaki Ofishin Yan sanda A Ebonyi, Sun kashe Jami’ai 3
NAN ta rahoto cewa PDP ta kuma lashe kujeru kansiloli 9 cikin 11 yayin da APC ta lashe sauran kujeru biyu.
A wani labarin Kuma na daban.
Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ce, a shirye yake ya yi aiki tare da Sanatan da ke wakiltar Kano ta Tsakiya kuma tsohon gwamnan jihar, Malam Ibrahim Shekarau, kafin shekarar 2023.
Ya kuma ce bai yi mamakin rikicin da ke ruruwa a jam’iyyar APC mai mulki a Kano tsakanin gwamna Abdullahi Umar Ganduje da sanatan ba.
Da yake magana a wata hira da BBC Hausa, jigon na Jam’iyyar PDP ya ce, “Duk wanda ba zai iya rama abubuwan alherin da aka yi masa tsawon shekaru ba, saboda shi da kansa (Ganduje) ya ambata cewa, mun yi abubuwan, Kuma mutane da yawa sun shaidan hakan.
“Amma lokacin da ya hau karagar mulki, ba zai iya yi wa Kwankwaso da mabiya Kwankwasiyya alheri daya ba. To ta yaya kuke tsammanin zaman lafiya zai kasance a wurin? Na san yana zuwa, lokaci ne kawai, ”in ji shi.
Da yake mayar da martani kan rahotannin da ke cewa Shekarau ya yaba masa, Kwankwaso ya ce, ya ji dadin kalaman.
Dangane da ko za su ci gaba da zama a sansanin siyasa ɗaya, Kwankwaso ya ce, ba zai yi mamaki ba domin idan Allah ya ƙaddara hakan ta faru, toh tabbas sai ta faru.
Tsohon ministan tsaro ya bayyana cewa, ya yi shiru a PDP saboda rashin adalcin da aka yi wajen zaben shugabanni a reshen Kaduna na jam’iyyar.
Ya Kuma Kara da cewa, bayan sun gudanar da zaben, wasu daga cikin shugabannin son kai sun yanke shawarar haifar da matsaloli ga shugabancin Kano, wanda a cewarsa, an warware su matsalolin daga bisani.
Amma ya ce, ya ci gaba da kasancewa dan PDP har izuwa wanna lokaci.
Idan za’a iya tunawa dai, Shekarau ya gaji Kwankwasoe a matsayin sanata mai wakiltar Kano ta tsakiya a majalissar Dattijan kasar nan.