An gurfanar da shugaban Jam’iyar PDP na yankin Igangan na Jihar Oyo mai suna Pa Olawuwo zuwa gidan fursuna sakamakon zargin shi da kisan wani mai suna Dakta Farai Aborode.
Rahotonni sun nuna cewa a jiya Alhamis ne aka chafke Olawuwo inda aka tusa keyar shi zuwa Sashen binciken miyagun ayyuka na CID dake Iyaganku a Birnin Badun.
Mai Magana da yawun rundunar Yan Sandar Jihar ya bayyana wa Jaridar Punch cewa bayan chafke da aka yi tuni kotu ta bada umarnin garkame shi a ofishin yan sanda.
Wata Majiya mai tushe ta bayyana wa Punch cewa wanda ake zargin da kuma wanda aka kashe dukkanin su daga mazaba guda suka fito.
To sai dai an haramta wa magoya bayan Olawuwo ganin shi yayin da suka daura damba zuwa gidan fursunar na yan sanda.