Yayin da Babban Zaben 2023 ke dada kara karatowa, An nada Tsohon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta takasa INEC Farfesa Attahiru Jega a matsayin shugaban Gangamin zaben gwamna a jam’iyar PRP na nan jihar Kebbi.
Sakataren yada labaran jam’iyar na jihar Abubakar Dakingari ne ya bayyana hakan a yayin taron masu ruwa da tsaki na jam’iyar da ya gudana ranar Asabar a dakin taro na Safar dake nan birnin Kebbi.
Yayin da yake bayhana Attahiru Jega a matsayin Shugaban tawagat, Dakingari ya kuma bayyana Dr Farouk Yahaya Abdullahi a matsayin Darakta Janar na yakin neman zaben Idris Udu.
Yayin da yake jawabi ga wadanda aka zaba, tsohon shugaban ma’aikatan jihar nan, kuma dan takarar gwamna a jam’iyyar PRP ana jiha, Alhaji Abubakar Udu Idris ya roke mambobin da su kasance masu gaskiya a tsakanin su.
A jawabinsa na karbar mukamin shugaban tawagar Farfesa Attairu Jega wanda ya yi jawabi ta kafar Zoom, ya yi wa masu ruwa da tsaki da ‘ya’yan jam’iyyar alkawarin yin aiki tukuru domin tabbatar da nasarar PRP a zaben shekarar 2023 dake tafe.
A wani labarin kuma na daban.
Kasar Indiya a ranar Litinin ta rantsar da sabuwar shugabar kasar Draupadi Murmu, wanda itace shugabar kasa ta farko data fito daga cikin kabilun kasar.
“Zaben da na yi ya tabbatar da cewa talakawa a kasar na iya yin mafarki da kuma cika su,” in ji ta bayan da ta yi rantsuwar kama aiki.
A Indiya, shugaban ya fi cika ayyukan wakilci, yayin da ikon gwamnati ya ta’allaka ne ga Firaminista.
Murmu, wacce ke cikin jam’iyyar Hindu mai kishin kasa ta BJP ta Firaminista Narendra Modi, ita ce mace ta biyu da ta taba rike mukamin.
‘Yan asalin ƙasar sun kasance kusan kashi 8.6 cikin ɗari na al’ummar Indiya kusan mutane biliyan 1.3 kuma galibi matalauta ne kuma marasa galihu.
Murmu wanda ta kasance tsohuwar malama ce, ta taba zama gwamnan yankin Jharkhand. (dpa/NAN