Jam’iyyar PRP za ta gudanar da taronta na kasa a ranar 11 ga Disamban shelarar, 2021.
Sakataren jam’iyar na kasa Alhaji Sule Kankara ne ya bayyana hakan a Katsina ranar Talata yayin da yake zantawa da manema labarai.
Ya ce an kammala shirye-shiryen taron.
Ya kara da cewa jam’iyyar ta sanar da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, da jami’an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki kan matakin gudanar da babban taron.
Kankara ya kuma bayyana cewa a yanzu jam’iyyar PRP tana da sabbin shuwagabanni a jihar Katsina bayan taron da aka yi a ranar Asabar da ta gabata.
KARANTA WANNAN LABARIN:Rundunar Sojin Mali ta Kubutar da Yan Kasar Sin da Aka saxe
A cewarsa, an gudanar da taron ne a garin Dandagoro dake karamar hukumar Batagarawa a jihar.
Ya Kuma ce an nemi ofisoshi goma sha daya a Majalisar zartarwar Jam’iyar a jihar, inda aka zabi Hassan Kankara a matsayin sabon shugaban jam’iyyar na jiha.
Kazalika ya ce, An zabi Mallam Lawal Rimaye a matsayin sakataren jam’iyyar na jiha yayin da Aisha Lawal ta zama shugabar mata a jihar ta Katsina.
Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai Farfesa Aliyu Jibiya daga Jami’ar Bayero, Kano; Alhaji Abdurrahman Abdallah, Malam Abu Yaradua, Alhaji Aliyu Tsauri da kuma Alhaji Musa Kankara.
Taron da jam’iyar ta gudanar ya Kuma samu halartar jami’an hukumar INEC a jihar da kuma jami’an hukumomin tsaro