Gabanin zaben gama gari, jam’iyyar Young Progressives Party (YPP) a jihar Filato ta narke cikin jam’iyyar, PDP. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
Bayan haka jam’iyyar YPP ta ce za ta goyi bayan ‘yan takarar jam’iyyar PDP a dukkan matakai a babban zabe mai zuwa.
KU KARANTA: Sam Emefele Bai Cancanci Zama Gwamnan CBN Ba – Inji Wani Gwamna
Shugaban jam’iyyar PDP na jihar Filato, Chris Hassan, ya karbi bakuncin shugabannin kananan hukumomin YPP 17 da suka shiga jam’iyyar a yayin da suke gudanar da harkokin siyasar jam’iyyar a karamar hukumar Mangu ta jihar.
Yayin da yake bukace su da su zabi jam’iyyar a duk zabuka, ya ce: “PDP ta shirya tsaf don zabe mai zuwa kuma PDP ce kadai ke da ninyar daga darajar jihar Filato kuma za ta yi kokarin kare al’adun Filato.”
Tun da farko a nasa jawabin, Ibrahim Adamu, wanda ya jagoranci shugabannin Jam’iyar YPP na kananan hukumomin zuwa PDP, ya ce jam’iyyar ta kafa wani kwamiti mai mutane 25 inda 22 suka amince cewa YPP ta hade da PDP.
“Daga yau, mun ruguje tsarin jam’iyyarmu zuwa PDP domin marawa Atiku Abubakar, Caleb Mutfwang da dukkan ‘yan takarar PDP baya a zabe mai zuwa,” in ji shi.
A wani labari kuma, Kin Amfan Tsofaffin Kudi: Zanga-Zanga Ta Barke A Ondo
Zanga-zangar ta barke a birnin Akure na jihar Ondo kan kin karbar tsoffin takardun kudi da bankunan kasuwanci suka yi. Kamar yadda The Nation ta ruwaito.
An fara zanga-zangar ne a bankin First Bank da ke Alagbaka, sakamakon fusatattun abokan huldan Banki da suka shafe sa’o’i da dama ba tare da zuwa wurin aikin ba.