Babbar jam’iyyar adawa ta Equatorial Guinea ta ce an samu kura-kurai a babban zaben kasar da aka gudanar a ranar Lahadin da ta gabata, inda shugaban da ya fi dadewa kan karagar mulki, shugaba Teodoro Obiang Nguema, ya nemi tsawaita wa’adin mulkinsa na shekaru 43.
Jam’iyyar mai suna Convergence for Social Democracy (CPDS) ta ce ba za ta amince da sakamakon zaben ba inda take cewa an tafka magudi kuma ba zata amince da duk wanda aka ayyana a matsyain zababben shugaban kasar ba.
KARANRA WANNAN LABARIN: 2023: Tinubu Na Da Dabarun Tsamo Najeriya Daga Matsin Tattalin Arziki, Jigon APC
A cikin wata sanarwa da ta fitar a jiya Lahadin jam’iyyar ta ce anyi magudu tare da tafka kura kurai a zaben daya gudana a fadin kasar in banda Malabo babban birnin kasar.
To sai dai hukumomin zabe da jam’iyya mai mulki ba su ce komai ba kan wadannan zarge zarge ba.
Ana ta bangaren jam’iyyar Convergence for Social Democracy (CPDS) ta ce jami’anta sun ga an tilasta wa masu kada kuri’a zaben yan takarar jam’iyyar Democratic Party of Equatorial Guinea (PDGE) ta shugaban kasar.
Haka kuma jam’iyyar ta ce an hana yan adawa sanya ido kan yadda za a kada kuri’a, ta hanyar abin da ta bayyana a matsayin yaudara.
Jam’iyyar ta kara da cewa, a rumfunan zabe da dama, jami’an zabe sun ba mutane damar kada kuri’a a madadin ‘yan uwansu da ba su zo runfunan zaben ba.
Kazalika ta yi Allah-wadai da kwace katunan zabe daga hannun masu kada kuri’a wadanda ta ce an ware su a matsayin magoya bayan ‘yan adawa.
Sai dai kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar The Convergence for Social Democracy (CPDS), Andres Esono Ondo, ya kuma yi zargin magudi da rashin bin doka a fadin kasar, ya na mai cewa, an hana mutane kada kuri’a cikin ‘yanci.
A wani labarin kuma, Buni Ya Kaddamar Da Tsarin Shirin Raya Kasa na Shekara 10 A Damaturu
Gwamna Mai Mala Buni na Yobe ya kaddamar da tsarin aiwatar da shirin raya kasa na shekaru 10 a Damaturu babban birnin jihar.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Alhaji Usman Geidam, Kakakin Sashen Yada Labarai na Yobe (YOGIS) ya fitar a Damaturu ranar Lahadi