Jam’iyyar ADC ta dakatar da dan takararta na gwamna a jihar Ribas, Tonte Ibraye da abokiyar takararsa, Tonto Dike, bisa zargin cin amana da rashin biyayya ga jam’iyyar Kamar yadda Daily Post ta rawaito.
Haka kuma an dakatar da tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar na jihar, Ode Lawrence-Gbagire, tsohon sakataren jam’iyyar na jihar, Eke Iheanyi-Eugene, tsohon shugaban matasa, Deinma Emmanuel, tsohon sakataren yada labarai, Luckyman Egila da tsohon mashawarcin shari’a, Hamza Victor-Chukere. .
KARANTA WANNAN LABARIN: An Sake Zabar Shugaban FIFA Gianni Infantino A Wa’adi Na Uku
Dakatarwar na zuwa ne kwanaki 2 gabanin gudanar da zabukan gwamnoni da na ‘yan majalisar jiha da za a yi ranar Asabar, 18 ga watan Maris, 2023.
A wata sanarwa da shugaban jam’iyyar na jiha, Sampson, mataimakin shugaban jam’iyyar, Alali Ikpoemugh da sakataren jihar, Gabriel Patterson-Unyeowaji, suka sanyawa hannu tare, dakatarwar ta biyo bayan shawarwarin da kwamitin ladabtarwa na jihar ya bayar wanda kuma kwamitin ayyuka na jihar ya amince da shi.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa dan takarar gwamna na jam’iyyar, Mista Ibraye tun bayan hawansa, “ya kara haifar da rarrabuwar kawuna a jam’iyyar, musamman ganin yadda ya amince da dan takarar shugaban kasa tare da abokin takararsa da kuma matafiya.
Sanarwar ta kuma ce dan takarar gwamna na jam’iyyar ADC da mataimakinsa, ba su nuna wani kuduri na yakin neman zaben gwamna mai zuwa ba, inda suka yi zargin cewa sun yi wa dan takarar kujerar Sanata a yankunansu.
Sun yi kira ga jama’a da su lura, domin mutanen da aka dakatar ba su da ‘yancin yin magana a jam’iyyar.
Da aka tuntubi Darakta Janar na kungiyar yakin neman zaben dan takarar ADC, Eke Eugene ya ce, “Sampson ba shi da ikon dakatar da su sakamakon dakatarwar da aka yi masa a baya daga jam’iyyar.”
A wani labarin kuma,Yanzu-Yanzu: ‘Yan Sanda Sun Cafke Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC
Abin da ya rage, kwana biyu a gudanar da zaben majalisar dokokin jihar Edo, mataimakin shugaban jam’iyyar APC na jihar, Jarret Tenebe, an kama shi bisa umarnin mataimakin gwamnan jihar, Hon. Philip Shaibu.
An ce an kama shi ne a garin Ikabigbo da ke karamar hukumar Etsako ta Yamma a jihar, saboda wasu dalilai da ba a bayyana ba.