Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ta fitar da Jadawalin ayyuka da jadawalin gudanar da zaɓukan shekarar 2023 mai zuwa.
Jam’iyyar ta ce an yi hakan ne bisa tanadin Dokar zaɓe ta shekarar 2022 kamar yadda aka yi mata kwaskwarima da kuma jadawalin hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa, INEC.
Idan za a tuna cewa, kwamitin Zartarwa na ƙasa na jam’iyyar APC ya yi taro, tare da mika iko ga kwamitin ayyuka na ƙasa na jam’iyyar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnatin Tarayya ta ki biyan Kungiyar ASUU Albashi
Bayan wannan cigaba ne Kwamitin zaɓe na APC, ya ƙayyade Naira miliyan 100 na fom domin tsayawa takarar Shugabancin ƙasa da kuma fayyace fam din takarar gwamna da ya kai Naira miliyan 50, sai Majalisar Dattawa Naira miliyan 20, sai kuma Majalisar wakilai Naira miliyan 10, da kuma na majalisar jiha akan Naira miliyan biyu.
To sai dai kuma duk da ƙorafin da jama’a da ɗaiɗaikun ƙungiyoyi da kuma ƴan takara ke yi, jam’iyyar mai mulki ta tsaya tsayin daka kan wannan farashi nata, inda a yanzu ta ke sa ran ganin zaɓen fidda gwani da sauran ayyukan da za ta yi kafin zaɓe.
Haka kuma jam’iyyar ta saki asusu guda bakwai daga bankunan Najeriya daban-daban inda ya kamata masu buƙata su fara yin ajiya.
Naƙasassu da mata da matasa masu shekaru 40 zuwa kasa, ba a sa ran su biya kudin fam din takara gaba daya.
Haka kima, Mata da nakasassu za su sayi fom ɗin Nuna sha’awa ne kawai, yayin da za su sami fom ɗin tsayawa takara kyauta.
Yayin da su kuma matasan za su biya rabin kudin fom na tsayawa takara tare da bayar da cikakken biyan kudin nuna sha’awar karbar fam