Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Adamu, ya gayyaci gwamnonin jam’iyyar APC zuwa wani taron gaggawa a ranar Lahadi.
Wannan ci gaban dai na zuwa ne biyo bayan takun-saka da yakin sunkuru da suka shiga yi tsakanin shugaban kasa, Muhammadu Buhari, da wasu gwamnonin da suka fusata kan batun sake fasalin kudin Naira.
KU KARANTA: Hukumar FA Na Tuhumar Arsenal Da Manchester City
Sake fasalin dai ya jefa ‘yan Najeriya da dama cikin mawuyacin hali a cikin dan wannan lokaci, kamar yadda jaridar Punch ta tawaito.
Jaridar ta kuma ruwaito yadda tarzoma ta barnata bankuna da kashe-kashe a jihohi da dama, musamman a jihohin Legas da Ribas da Ogun da kuma Edo.
Sa’o’i kadan bayan watsa shirye-shiryen shugaban kasa, Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya yi jawabi ga mazauna Kaduna, inda ya ce tsohon shugaban kasar na mulkin soja bai yi kuskure ba a kan umarnin da ya bayar na sake raba tsofaffin takardun kudi na Naira 200 kawai a matsayin wani mataki na dakile tabarbarewar kudi a kasar.
A wani labarin kuma: Alkawarin da kuka yi na zaben gaskiya da adalci a Imo – PDP
Jam’iyyar PDP a jihar Imo a ranar Juma’a ta bayyana cewa ya kamata shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fahimci cewa alkawarin da ya dauka na baiwa ‘yan Najeriya zabe na adalci zaici tura a jihar Imo.
Collins Opurozor, Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar PDP ne ya bayyana haka a Owerri a lokacin da yake zantawa da ‘yan jarida kan halin da kasa ke ciki, hari na uku da aka kai wa kakakin jam’iyyar CUPP, Ikenga Ugochiyere a gida, da kuma kashe-kashen wadanda ba su ji ba ba su gani ba a gidan sa.