Tsohon Mataimakin shugaban Ƙasa Atiku Abubakar yace Najeriya na fama da wani matsanancin hali, musamman ta fuskar yanda ƙasar ke fama da tsayawa da duga-gudanta.
Ya bayyana haka a ranar Asabar a lokacin zaɓen shuwagabannin jamiyyar PDP na Ƙasa na shekarar 2021, wanda ya wakana a filin taro na Eagle Square dake Abuja.
Wazirin Adamawa yayi kira ga mambobin jami’iyyar, da dukkanin ƴan Najeriya dasu jefar da bambance-bambance, tare da lura akan siyasa gami da bada ƙoƙari wajen fitar da jamiyyar APC daga mulki.

KARANTA WANNAN LABARIN: Hukumar Kashe Gobara Ta Jihar Kano Ta Ziyarci Sansanin Masu Yiwa Kasa Hidima Dan Gangamin Wayar Musu Da Kai
Yace Jami’iyyar APC ta kasa yiwa ƴan Najeriya abinda ya kamata na tsawon shekaru 6, amma har yanzu akwai damar gyara kura-kuran da Shuwagabannin da suka wuce suka yi, gami da haɗa kan ƙasar domin samun cigaba.
Yace “zan iya gaya maku cewa shekaru na 70 da ɗoriya, amma ban taɓa ganin ƙasar nan a cikin wani mummunan hali, da rabuwar kai, da rashin aikin yi, gami da taɓarɓarewar tsaro a tarihin ta, kamar yanzu.
“Matsalolin tsaro a ko’ina gami da tashin hankali na haɗin kan ƙasar, Najeriya na cikin wani hali na lalacewa, gami da taɓarɓarewar ƙwazon gwamnatocin da suka gabata, wanda hakan ya haddasa faɗuwar jamiyyar APC ƙasa warwas.
“Jam’iyyar APC ta nuna cewa ba zata iya jagorantar ƙasar nan ba. Sun nuna cewa maciya hanci ne, a taƙaice sunfi kowa cin hanci, da ɓangaran ci, wargazazzar jam’iyyar da bazata iya jagorantar ƙasar nan ba.
“Abinda ke garemu shine na magance lalacewar ƙasar daga duk wani bala’i, Wannan shine aikin mu gaba ɗaya.
Atiku ya ƙara dacewa “Dole mu ajiye bambance-bambance . Dole muyi amfani da mukamin mu, domin gina ƙasar nan.
“Wannan shine lokacin da ƴan siyasa ya kamata suyi aiki tuƙuru domin dawo da Najeriya turbar kawo cigaba a ƙasar.
Comments 1