Tsohon gwamnan jihar Kano kuma tsohon ministan Ilimi, Sanata mai wakiltar Kano ta tsakiya, Malam Ibrahim Shekarau ya ce yana nan daram a jam’iyyar APC har sai sun tabbatar da saituwar al’amura.
Sanata Shekarau ya bayyana hakan a yau Talata yayin wani taro da kwamitin Shura na G7 da ya gudana a gidansa dake Mundubawa a jihar Kano.
“Tun bayan zaben shekarar 2015 ba a nemanmu kan duk wani al’amari na jam’iyya ko mukamai za a bawa bangarenmu ba a tuntubarmu.
” Muna nan Daram a APC, sai mun kwatowa ‘yan jam’iyya hakkinsu, idan a ka zabi shugabanni bara gurbi, shekara 4 za a yi ana gasawa mutane aya a hannu.”
Tsohon gwamnan ya kuma bayyana yadda Sanatan Kano ta kudu, Kabiru Gaya ya ci amanarsu bayan tattaunawa da suka zauna suka yi a tsakaninsu.
“Taron da muka yi a Abuja, Kabiru Gaya ya kwashe labarin ya fadawa Gwmana da Abdullahi Abbas.”
Malam Ibrahim, Shekarau ya musanta cewa suna rigima ne domin sake tsayawa takara, ya ce suna yi ne domin ceto jam’iyyar APC.
Da yake hira da manema labarai, tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano, Farfesa Hafiz Abubakar ya bayyana cewa yana tare da bangaren Sanata Shekarau, ya ce akwai rashin adalci kan yadda ake tafiyar da jam’iyyar APC a Kano, “Matsayata ita ce, ina alakanta kaina da gaskiya da kuma nan duba nan gaba. Maganar gaskiya ita ce abinda ke faruwa a APC ba abu ne mai dadi ba.
A yau kowa ya sani cewa shugabanni a APC suna shiga taron jama’a suna cewa jam’iyya ta mutum gwamna da matarsa da shugaban jam’iyya.
” Wasu lokutan muna ganin hakan abin dariya amma abinda muke gani a aikace yana nuna zahirin abinda ke faruwa. Jam’iyyar APC a Kano ta zama koma baya. Don haka yana daga cikin aikinmu mu ceto jam’iyyar mu ceto kanmu sannan mu ceci al’ummar Kano.
Taron ya samu halartar dubban magoya bayan jam’iyyar APC da shugabanni a jam’iyyar tsagin Sanata Ibrahim Shekarau.