Jam’iyyar APC za ta fara saida tikitin takara
Jagororin jam’iyyar APC na shirye-shiryen fara sayar da tikitin takara a farkon watan Juli. Kamar yadda Jaridar Vanguard ta ruwaito.
Farfesa Mustapha Medaner, shugaban shirye-shiryen na jam’iyyar APC, ya bayyana haka ga manema labarai a Abuja.
Medaner yace ” hakan ya biyo bayan kaddamar gwamna Mai Mala Buni a matsayin Jagoran jam’iyyar APC na wucen gadi, da sauran wasu jigajigan APC.”
KARANTA:- Ku gama zumudinku jam’iyyar APC ba za ta wuce 2023: Inji PDP
Ya cigaba da cewa” za’a fara saida tikitin gundumoni a daya ga watan Juli zuwa bakwai.”
Madener ya kuma sanar da jadawalin ayyukan jam’iyyar tun daga matakin gunduma da kananan hukumomi.
Ya kara da cewa tantance yan takara zai soma ne a Sha biyu zuwa Sha shida duk a watan Juli.
Sannan za’a bada damar kawo korafe-korafe ne a ashirin da shida zuwa ashirin da tara ga watan Juli.
Jagororin gundumomi zasu sayi tikitin akan dubu 10, sannan sakatarori da ma’aji dubu 5, sauran wakilan zasu saya akan dubu biyu.
A inda shugaban Karamar Hukuma zai saya tikitin takarar sa akan dubu 25,000, mataimakin Shugaban Karamar Hukuma da sakatarori da kuma ma’aji dubu 15,000. Sannan sauran wakilan dubu 10,000.
Madener ya kuma ce ” Masu sha’awar tikitin daga cikin Mata da masu tawaya za su biya kaso 50 cikin kudin da aka kayyade.
Comments 1