Kungiyar Kwadago ta Ƙasa NLC, ta shaidawa wakilan jam’iyyar Labour Party, LP, a zaben fidda gwani na jam’iyyar a Asaba, jihar Delta, cewa ‘yan Najeriya na sa ran LP zata kawo sauyi da ceto kasar daga talauci.
Baya ga haka suna saka ran cewa jam’iyyar zata ceto Najeriya daga matsalar rashin tsaro, da rikice-rikicen cikin gida da sauran kalubalen da take ci gaba da fuskanta ta kowace Fuska.
Shugaban NLC, Ayuba Wabba a cikin wani sako da ya aikewa Deliget din jam’iyyar a taron fidda gwanin da ke gudana a Asaba, ya bukaci wakilan da su zabi ‘yan takarar da suka amince da “Sauke hakkin Ma’aikata da biyan Bukatun su”, yana mai jaddada cewa “ya kamata wakilai su yi taka-tsan-tsan da ’yan takarar da ke bakin kokarinsu na ci gaba.
Wabba ya ce, “Ya kamata a yi la’akari sosai ga ’yan takarar da tarihinsu ya nuna rashin jin dadi, kamun kai, mutunci da kuma tsarin kasafin kudi.
Muna son wakilai su zabi ’yan takara masu goyon bayan Najeriya da masu goyon bayan ma’aikata da kuma wadanda za su hada kan kasar.
“Ba lallai ne ’yan takararmu su zama yadda aka so su zama ba, amma ’yan kishin kasa ne, wadanda za su mayar da duk wani kobo da Najeriya ta samu a matsayin kudin shiga tare da aiki da su zuwa ayyuka masu muhimmanci da za su daukaka kasa baki daya,” Inji Wabba.