Jam’iyyar PDP bazata Ƙara Karɓe Mulki a Ebonyi, APC tasha Alwashi
Jam’iyyar APC a ranar Asabar ta sha alwashin hana Babbar Jam’iyyar Hamayya ta PDP sake karɓe Jahar Ebonyi.
Jam’iyyar tace tana da shirin ƙwace Jahohi guda 5 na yankin Kudu Maso Gabas a Babban Shekarar 2023 farawa daga Jahar Abia da Enugu.
KARANTA WANNAN LABARIN: Osun: Kotu ta Ɗaure Tsohon Kwamandan Matasa Masu yiwa Ƙasa Hidima Shekaru 2 kan satar 3.1m
Mataimakin Shugaban Jam’iyyar na Ƙasa na Yankin Kudu maso Gabas, Dr Ijeomah Arodiogbu ya bayyana haka a lokacin ƙaddamar wa na Shiyya a ofishin Jam’iyyar na Shiyya a Enugu.
Arodiogbu a lokacin da yake jawabi ga Ƴan Jarida ya bayyana gamsuwar sa da hukuncin da Kotun Ɗaukaka Ƙara a Enugu tayi wanda ya kori Ƙarar da aka shigar na cire Gwamnan Ebonyi Chief David Umahi.
Yace Jam’iyyar na farin ciki da hukuncin, tana mai cewa wannan wani aiki ne na kare dukkanin Jahohi dake ƙarƙashin Jam’iyar a yankin.
“Ebonyi na ɗaya daga cikin Jahohi, kuma bazamu bari mutane su fito daga bayan ƙofa, tare da neman cin mutuncin Gwamna” Cewar Arodiogbu.
Arodiogbu ya cigaba da cewa ofishin Jam’iyyar na Shiyya tana da ƙudiri a Shekarar 2023 wanda shine samun nasarar lashe dukkanin Jahohi dake yankin Kudu maso Gabas, yana mai ƙara dacewa hakan bazai samu nasara ba sai da goyon bayan Al’umma.