Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya gargadi takwaransa na jihar Rivers, Nyesom Wike, da kada ya kawo cikas a jam’iyyar PDP, tare da tabbatar da cewa dukkan mambobi daidai suke a karkashin wannan jamiyya.
Rikicin dake tsakanin Gwamnan Jihar Edo Godwin Obaseki da abokin hamayyarsa Gwamanan jahar Rivers Nyesom Wike yayi tsamari a jiya.
Gwamnan Jihar Edo Obaseki yace bazai lamunci tsangwamar siyasa tare da tunawa Wike yadda ya cire Shuwagabanni masu tsangwama akan siyasa.
A cikin wata takarda an jiyo Gwamnan Jihar yana tuhumar Wike da wasu halaye Marasa inganci kuma yana kira da Jam’iyyar da tayi kira a gareshi da ya gyara.
Yayin kare mataimakin sa akan nuna ra’ayin sa akan Jam’iyyar PDP a Edo, Obaseki yace Wike ya dauki alama kamar yadda Ciyaman din kasa yayi Dr. Iyorchia Ayu, ya bada amsa ga ra’ayin Shu’aibu.
Ya yi bayanin korafin Shu’aibu da cewa “Shuwagabanni, Jami’an zartarwa tare da mambobin da suka yi Mulki tare a Jam’iyyar APC basu samu karbuwa ba zuwa Jam’iyyar PDP a Jihar Edo.
Obaseki yana mamakin yadda Wike yake yawan barazana ga Shuwagabannin Jam’iyya da Jam’iyyar baki daya. Yace bayan ba wanda yake Sukar ra’ayin Wike na tsaya wa takarar Shugabancin kasa Kada ya nemi abinda yake so ta hanyar da bata dace ba.
Obaseki yace “Tunda Wike yana da ‘yancin amfani da arzikin sa domin samun cikar burin sa, ka da yayi yunkurin dakatar da kowa ko kuma barazana ga wasu yayin gudanar da ra’ayin sa. Jahar Edo bazata iya samuwa ba domin cikar burin wani.