Rikici ya ɓarke tsakanin jam’iyyar adawa ta PDP da APC mai mulki kan sabbin manufofi tara da Shugaba Buhari ya ce gwamnatinsa ta sa a gaba.
A ranar Talata Buhari ya bayyana jerin abubuwan da gwamantinsa za ta ba wa muhimmanci a shekara ukun da suka rage masa, da suka haɗa da samar da ingataccen ilimi da kula da lafiya da wutar lantarki da rage talauci da sauransu.
Jam’iyyar PDP a wani saƙo da Sakataren Yada Labaranta, Kola Ologbondiyan ya fitar ta ce shekaru biyar bayan hawan mulkin Buhari bai daina alkawari ba duk cewa ba ya iya cika su, alhali takwarorinsa a wasu ƙasashe ke bajekolin nasarorinsu.
Ologbondiyan ya ce akwai yaudara a cikin sabbin maufofin Buharin wanda bai cika alƙawuran zaɓen da ya yi a wa’adinsa na 2015 zuwa 2019 ba na yaƙi da rashawa da farfaɗo da tattalin arziki da kuma samar da tsaro”, cewar Sakataren Jam’iyyar PDP.
Ya ƙara da cewa, “Ya kamata duniya ta tuna cewa Shugaban ƙasa da jam’iyyarsa ta APC sun yi wa ’yan Najeriya romon baka suka zaɓe su amma da suka ci zaɓe sai suka juya wa ‘yan Najeriya baya.
“Shugaba Buhari da APC sun yi alƙawarin biyan marasa aiki albashin N5,000 da samar da ɗimbin ayyuka da gidaje kyauta da kuma alawus a duk wata ga matasan da suka kammala yi wa ƙasa hidima.
“Sun kuma yi alƙawarin rage farashin mai da farfaɗo da matatun mai tare da mayar da darajar Naira daidai da na Dala da sauran alƙawuran da a yaunzu sun zama shafcin-Gizo.
“Bayan hawa Mulki, Buhari ya rage alƙawuran nasa suka koma guda uku da suka haɗa da yaƙi da ta’addanci da samar da tsaro, yaƙi da rashawa da farfaɗo da tattalin arziki”.
https://dimokuradiyya.com.ng/pdp-ta-nemi-buhari-ya-yi-murabus-saboda-matsalar-tsaro/
“Sanin kowa ne cewa Shugaba Buhari ya gaza a duk alƙawuran guda uku da yake iƙirarin ya ɗauka.
“A shekara biyar na mulkin Buhari matsalar tsaro ta tsananta fiye da kowane lokaci da ’yan fashin daji, masu tayar da ƙayar baya da masu garkuwa da mutane a birane da ƙauyuka, ciki har da mahaifarsa wato jihar Katsina”, inji PDP.
A martaninsa, Mataimakin Kakakin Jam’iyyar APC na ƙasa, Yekini Nabena ya ce yanzu “wala-wala a tattalin arziki da rashin kammala ayyuka da cuwa-cuwa” duk sun fi yawa a zamanin PDP.
A matsayin PDP na jam’iyyar adawa a yanzu, abin kunya ne ta riƙa ambaton munanan abubuwan da ya ce gwamnatin PDP ta yi na yaɗa cuwa-cuwa.
“Ɓata lokaci ne magana da PDP bayan gwamantinta ta gaza yanzu kuma sun rasa alƙibla a matsayin jam’iyyar adawa.
“Abin da ya fi fitowa shi ne, kar a ƙara bari Jam’iyyar PDP ta mulki ƙasar nan.
Ɓangarorin da Shugaba Buhari ya ce zai ba wa muhimmanci su ne samar da ilimi mai nagarta da wutar lantarki tsayayya da kuma kiwon lafiya managarci da rahusa.
Akwai kuma samar da tattalin arziki mai ɗorewa da inganta masana’antu da kuma ba wa jama’a dama da yaye talauci.
Ya ce zai kuma inganta sha’anin noma domin samar da wadataccen abinci har a riƙa fitarwa da kuma samar da ingantaccen sufuri.
Sannan ya ƙara da cewa zai ɓullo da hanyoyin yaƙar rashawa baki ɗaya da kuma inganta harkar tsaro.