Jam’iyyar PDP ta goyi bayan tsohon shugaban ƙasa Obasanjo tare da wasu manyan ƙasar nan dangane da fitowa fili su faɗawa gwamantin ƙasar nan gaskiya dangane da halin matsi da ‘yan Najeriya suka tsinci kai a ciki.
Wannan ya fito ne a wani jawabi da shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa Uche Secondus, mai magana da yawunsa ya sanyawa hannu, Ike Abonyi yace “ya kamata gwamnatin nan ta rungimi gaskiya”.
Ya yabawa Obasanjo da cewa “abun a yaba masa ne wajen faɗar gaskiya a duk lokacin da wani abu yake tafiya ba daidai ba”.
Secondus ya ƙara da cewa ya kamata gwamnatin Buhari ta amince cewa ta jefa Najeriya cikin wani matsanancin hali.
Ya ƙalubalanci gwamnatin ta Buhari kan sukar duk wani da yake faɗar gaskiya akan gwamnatinsa.
Sannan ya sake jan hankalin Buhari da ya bada umarnin yin sahihin zaɓe a jihar Edo.