Kwamitin gudanarwa na Jami’iyyar PDP ya sake dage ranar gudanar da zaben fidda gwani na jam’iyyar.
Sakataren wayar da kan jama’a na Jam’iyyar a jihar Legas Mr Hakeem Amode ne ya sanar da hakan, cikin wata Sanarwa da aka rabawa manema labarai a yau Juma’a.
Wannan dagewar dai ba shine na farko ba da jam’iyyar tayi, kuma hakan na zuwa ne a daidai lokacin da babban zaben 2023, yake kara karantowa.
A cewar sanarwar yanzu zaben fidda gwanin na yan majalisar wakilai ya koma 22 ga watan Mayu, maimakon 21 ga watan Mayu.
Yayin da Zaben sanatoci yake a ranar 23 ga watan Mayu, sai na Gwamnan shima da ba a sauya shi ba, yana nan a 23 da 26 ga watan Mayu.
Zaben na shugaban kasa kuwa an sanya ranar 28 da 29 ga watan Mayu, kamar yadda sanarwar ta bayyanar.