Jam’iyyar PDP ta shirya gagarumin taronta na shiyyar Arewa maso Yamma domin zabar kwamitin gudanarwa na shiyyar da kuma tsoffin jami’an shiyyar a ranar Asabar 12 ga watan Fabrairu.
Jam’iyyar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da sakataren jam’iyyar na kasa, Umaru Bature, ya fitar ranar Alhamis a Abuja.
Ta bayyana cewa matakin na daga cikin kudurin da kwamitin ayyuka na jam’iyyar PDP na kasa (NWC) ya yanke a taron da ya yi a ranar Laraba.
Ya ce an shirya gudanar da taron shiyyar Arewa maso Yamma a shedikwatar jam’iyyar a jihar Kaduna.
“Dukkan masu ruwa da tsaki da kuma jiga-jigan jam’iyyar mu a shiyyar Arewa maso Yamma sun sanar da hakan kuma an yi musu jagora yadda ya kamata,” in ji jam’iyyar. (NAN)