By Abbas Yakubu Yaura
Jam’iyyar PDP ta taya tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan murnar bikin cikar sa shekaru 64 a duniya.
Jam’iyar ta bayyana hakanne Aacikin wata sanarwa da sakataren yada labaran sa na kasa, Kola Ologbondiyan ya fitar, yace sadaukarwar da Dakta Jonathan ya yi na kashin kansa wajen tabbatar da hadin kai da zaman lafiyar al’ummar kasa, musamman bayan zaben shekara ta 2015, ya sanya shi fice a matsayin dan takarar da ya sanya rayuwar al’ummar kasar nan sama da son rai.
Sannan ya ce jam’iyyar PDP da ‘yan Nijeriya a duk fadin kasar nan suna alfahari da tsohon shugaban kasar a matsayinsa na shugaba na musamman mai kishin kasa kuma jigon kasa wanda nasarori da sadaukarwar da ya yi wajen tabbatar da hadin kai da zaman lafiyar al’ummar kasar nan sun kasance ba su gushewa a tarihin Nijeriya.