By Abbas Yakubu Yaura
A ranar Juma’a ne kwamitin ayyuka na jam’iyyar PDP ya amince da tsawaita wa’adin kwamitin riko na shiyyar Arewa maso Yamma da kuma kwamitin riko na jihar Legas na tsawon kwanaki 30.
Sakataren yada labarai na jam’iyyar na kasa, Debo Ologunagba, ya bayyana hakan a wata sanarwa mai taken ‘PDP ta tsawaita wa’adin shiyyar Arewa maso Yamma, kwamitocin riko na jihar Legas.
Ologunagba ya ce, “Kwamitin ayyuka na kasa na babbar jam’iyyar mu, jam’iyyar PDP ta amince da tsawaita wa’adin kwamitin riko na shiyyar Arewa maso Yamma da kuma kwamitin riko na jihar Legas na tsawon kwanaki 30.
“Don haka, mambobin kwamitocin riko na yanzu za su ci gaba da gudanar da ayyukansu na karin tsawon kwanaki 30, bayan karewar wa’adin da suka yi a yanzu.
“Saboda haka, an tsawaita wa’adin kwamitin riko na shiyyar Arewa maso Yamma daga ranar Litinin, 28 ga watan Fabrairu, 2022 zuwa Litinin 28 ga watan Maris, 2022 yayin da kwamitin riko na jihar Legas kuma aka kara wa’adin aikin sa daga ranar Asabar 19 ga watan Fabrairu zuwa 2022. Asabar, 19 ga watan Maris 2022.”
Sakataren jam’iyyar ya bukaci duk masu ruwa da tsaki da ‘ya’yan jam’iyyar PDP na shiyyar Arewa maso Yamma da kuma jihar Legas su lura da karin wa’adin.