Jam’iyyar PDP za ta Ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman Zaɓen Shugaban Ƙasa
Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta ce nan ba da dadewa ba zata bayyana jerin sunayen kwamitin yaƙin neman zaɓen Shugaban Ƙasa na 2023.
Sakataren yada labarai na kasa Debo Ologunagba ya bayyana haka ga Manema Labarai a daren Laraba bayan wani taron kungiyar ‘yan Majalisar Tarayya a Abuja.
KARANTA WANNAN LABARIN: Majalisar Dokokin Bauchi ta umarci Gwamna Bala yayi Gaggawar gyara hanyoyin da Ambaliyar Ruwa ta shafa
Kakakin ya bayyana cewa Kwamitin Amintattu (BoT) da Majalisar Zartarwa ta Kasa (NEC) za su gana kan jerin sunayen.
“Jam’iyyar ta shirya tsaf domin gudanar da zabe. An warware dukkan batutuwa.
“Mun shirya tafiya. Mun shirya. Bangarorin jam’iyyar suna aiki.”
Ologunagba ya ce ‘yan adawa sun shirya aikin ceto Najeriya, kuma za su sake gina kasar idan aka zabe su a 2023.
Ya bayyana cewa wasu gwamnonin PDP ba su halarci taron ba saboda wasu sun yi hutu amma suna da wakilci.
A wani labarin kuma: 2023: Kasawar APC ba zai sa Gwamnonin PDP da basu yi aiki su samu Ƙuri’u ba — Wike
Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike, ya ce zai zama kuskure ga Gwamnonin jam’iyyar PDP, da suka kasa samar da shugabanci na gari a jihohinsu na neman kuri’u daga masu zabe.
Ya bayyana hakan ne a wajen bikin kaddamar da harabar jami’ar Emohua na jami’ar jihar Ribas, da kuma kaddamar ds rukunin gidaje ga ma’aikata, wanda gwamnan jihar Oyo Seyi Makinde ya yi a ranar Laraba.