Jam’iyyar PDP Mai adawa a Kasar nan za ta shiga wani dakin tantance yan takarar ta na gwamna a Jihar Anambra a ranar Litinin 12 ga watan Maris don fitar da dan takara daya tilo da zai fafata mata a zaben gwamna dake tafe.
Tantancewar dai za ta kasance ne karkashin shugabancin Tsohon gwamnan Jihar Kogi Idris Wada, daga ranar Litinin zuwa talata da Misalin karfe tara na safe.
Idris Wada ya ce suna fata yan takarar za su nuna halin Dattaku ta hanyar bin dokokin jam’iyyar sau da kafa ba tare da muna-muna ba.
Shi dai wannan zabe na gwamnan a Jihar ta Anambra zai Gudana ne a Ranar 6 ga watan Nuwamban wannan shekara kamar yadda hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta tsara.