By Abbas Yakubu Yaura
Jam’iyyar SDP, za ta kwace ikon siyasa a jihar Kwara a zaben 2023, in ji shugaban jam’iyyar na jihar, James Dada a ranar Litinin.
Ya bayyana cewa tare da sabbin ‘yan jam’iyyar da suka samu mafaka daga manyan kusoshin adawa a cikin rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar APC, a kwanan baya, jam’iyyar ta ci gaba da habaka da kuma kara karfi a jihar.
Dada ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a ofishin kungiyar kwadago ta Najeriya NLC, dake Ilorin a titin Lanjorin inda ya gudanar da taron sanin makamar aiki da jami’an kasa da na jiha.
Da yake jawabi a wajen taron, shugaban jam’iyyar na jihar, ya ce jam’iyyar SDP ta zo ta zauna a Kwara.
Jihar Kwara na daya daga cikin Jiha da SDP ta samu gindin zama tare da dimbin ‘ya’yanta.
“Ya zama dole a bayyana a nan ba tare da faɗi kalmomi ba cewa wasu masu hannu da shuni sun gamsu da tsarin jam’iyyar kuma sun amince da yin aiki tare da mu a kan wannan hanya,” in ji shi.
A cewar jigon jam’iyyar, SDP ta rage yawan mambobinta a kananan hukumomi 16 da ke fadin jihar.
Kazalika Dada ya bayyana cewa baya ga ’ya’yan jam’iyyar APC masu ra’ayin rikau, yanzu suna cikin jam’iyyar, ‘ya’yan jam’iyyar PDP suma sun nuna aniyarsu ta shiga jam’iyyar SDP.
Ta haka ne taron na yau ya nuna cewa jam’iyyar SDP ta zo kuma da yardar Allah za ta mulki jihar a 2023,” inji shi.
A kwanakin baya ne dai wani bangare na jam’iyyar APC mai biyayya ga ministan yada labarai, Lai Mohammed, ya sauya sheka zuwa jam’iyyar SDP a birnin Ilorin.
Comments 1