Hukumar zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa INEC ta ce a halin da ake ciki ba za ta wuce gona da iri ba dangane da abinda ya shafi Jam’iyyun siyasa, don haka za ta ci gaba da aiki ne da jam’iyyu 18 da aka yi wa rejista duk da cewa akwai korafe-korafe da ke gaban kotun koli.
Cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar a yau Juma’a dake dauke da sanya hannun Kwamishinan hukumar taq kasa kana Shugaban Kwamitin Wayar da Kan Jama’a Kan harkokin masu zabe Festus Okoye, ta bukaci sauran Jam’iyyu 74 da ba a yi wa rejista ba da su jinkirta har zuwa lokacin da kotu za ta yanke hukunci kan karfin ikon INEC na cire sunayen sauran jam’iyyu daga bayanan ta kamar yadda sashe na dari biyu da hamsin da biyar na kundin tsarin mulkin hukumar ya tanadar.
Hukumar ta kara da cewa ita mai biyayye ce ga umarnin kotu don haka ba za ta yi riga Malam Masallaci ba har sai hukuncin Kotun ta yanake.
INEC din ta kuma kafe kan cewa ba za ta bada dama wa wata jam’iyya da ba ta da rejista ba kan cewa ta gudanar da zaben cikin gida, ku,a ba za ta karbi takardar ko wane dan takara da aka zaba a yayin zaben cikin gidan ba.
Bugu da kari sai ta gargadi sauran jam’iyyu da aka yi wa rejista da kada su kuskura su karye dokar cikin gida ta jam’iyyar su kana su smar da ita kai tsaye wa hukumar.
Ta Kara da cewa bin dokokin jam’iyya sau da kafa shine hanya mafi suaki na dabbaka dimokuradiyya, don haka kada su yi skaaci wajen tanadar da dokar su kamar yadda yake cikin dokokin dimokuradiyya.