Jam’iyyun siyasa 18 ke neman kujerar Gwamnan Jihar Sokoto
A kalla jam’iyyu 18 ne za su fafata a zaben gwamna a jihar Sakkwato, kamar yadda hukumar zaɓe mai zaman kanta ta bayyana a ofishinta da ke Sokoto.
A karon farko Jam’iyyu guda biyu sun sanya ƴan takarar mataimakan Gwamna mata.
KARANTA WANNAN LABARIN: Matsalar Tsaro: Ka Gaggauta Yin Murabus, Shugaban Jam’iyar NNPP Na Katsina Ga Shugaban Kasa Buhari
Sun hada da Hannatu Muhtar wadda ita ce mataimakiyar ‘yar takarar gwamna a dandalin jam’iyyar Action Peoples Party da Hauwa’u Bello wadda ita ce mataimakiyar ta Jam’iyyar Allied Peoples Movement.
A yayin da wakilinmu ya ziyarci ofishin INEC, baya ga ’yan takarar jam’iyyar All Progressive Congress and Peoples Democratic Party, suna da Saidu Umar da Ahmed Aliyu Sokoto.
Sauran sun hada da Isiyaku Bello na ADC, Abubakar Haruna na APM, Habibu Muhammed na Zenith Party, Ibrahim Muhammed Mansur Gada APGA da Goronyo Ibrahim na Boot Party.
Akwai kuma Dahiru Umar Tambuwal na NNPP, Muhammad Saidu Gumburawa na PRP, Daniya Usama Sani na YPP, Imam Abdulrahim Chindo na Labour Party yayin da National Rescue Movement ta gabatar da Aliyu Sulaiman DanDauda.
Action Alliance ta gabatar da Ahmad Ahmad Jao, ADP na da Nasiru Sarki Larabawa, SDP na da Umar Abdul-Razak, African Action Congress tare da Ahmad Babajo Ibrahim da Abba Sidi Ahmed ga Jam’iyyar Action Peoples Party.