Kasar Jamus ta nada kocin Bayern Munich daje ƙasar Hansi Flick a matsayin sabon Kocin ta wanda zai kasance gar zuwa shekara ta 2024.
Darkatn wasanni na Kasar ta Jamus Oliver Bierhoff ya sanar sa haka a yau talata inda ya ce da ma ya jima yana tsumayin wannan rana.
Da ma dai a watan Afirelun da ya gabata ne Flick ya sanar da muradinsa na ajiye aikin horas da Bayern Munich inda tuni aka maye gurbin sa da kocin RB Leipzig Julian Nagelsmann.
A shekara ta 2014 ne Flick ya yi ajiye aiknsa da Jamus sa’ilin da suka lashe kofin duniya bayan shafe shekara takwas yana Mataimaki wa Joechim Low da ya ajiye aiki a bana.