Kasar Jamus na kokarin janye takunkumin hana shiga kasarya da ta kakaba wa kasar Birtaniya da wasu karin ƙasashe huɗu.
A ranar Laraba ne ake sa ran kasar za ta janye takunkumin wa kasashen da suka hada Portugal da Rasha da Indiya da kuma Nepal saboda sabon nau’in cutar korona da ta bulla a kasashen.
Jamus din ta ce duk matafiyin da aka yi wa rigafin cutar to ba za a killace shi ba kamar yadda aka saba.
Sai dai ta ce duk wanda bai karbi rigafin ba, to lashakka za’a killace shi har ma tsawon kwanaki goma.
Ko da yake da ma dokar ba ta hau kan yan kasar Jamus din dake komawa gida ba, amma an ve tilas ne idan suka dawo a killace su har na tsawon kwanaki 14 idan suka shigo.