Babban hafsan hafsoshin tsaron kasar Janar Lucky Irabor, ya ce akwai bukatar a samar da kwakkwarar hadin gwiwa tsakanin dakarun sojin Afirka ta Yamma, domin tunkarar matsalar rashin tsaro a yankin.
Irabor ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin babban hafsan hafsan sojin Burkina Faso, Senior David Kadre a shedikwatar tsaro ranar Alhamis din nan a Abuja.
Ya taya babban hafsan tsaron Burkina Faso, wanda tsohon dalibi ne a kwalejin tsaro ta kasa (NDC) Najeriyar bisa nadin da aka yi masa tare da ba da tabbacin yadda kasashen biyu ke tunkarar matsalar rashin tsaro.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Irabor ya ce Najeriya ta yi alfahari da samun tsohon dalibin NDC ya zama babban hafsan tsaro na Burkina Faso, yana mai jaddada kudurinsa na taimakawa juna da maziyartan.
KARANTA WANNAN: https://dimokuradiyya.com.ng/hukumar-fansho-ta-soja-ta-biya-mafi-karancin-albashin-maaikata/
“Babu shakka yankin yammacin Afirka na fuskantar barazanar ta’addanci da tada kayar baya kuma mun fahimci cewa domin magance wannan annoba, dole ne a samar da hadin gwiwar dukkanin kasashen yankin.
“Don haka na yi farin cikin tarbar ku kuma in sanar da ku cewa za mu raba abubuwan da muka samu.
“Hakika za mu dauki matakin da zai tabbatar da cewa mun gyara dukkan al’amura tare da tabbatar da cewa mun kawar da duk wani nau’in ta’addanci a yankinmu,” in ji shi.
Tun da farko, Kadre ya ce ya je Najeriya ne domin halartar bikin yaye gurbin karatu na Course 30 na NDC Nigeria, kuma ya yi amfani da damar da ya kai ziyara ga Irabor domin ya samu ilimi da kwarewa.
Kadre ya ce ya kuma ki ziyarar ne domin neman shawarwari kan sabon nadin nasa da kuma gabatar da batun tsaro a yankin yammacin Afirka.
Ya nanata bukatar kara zurfafa hadin gwiwa tsakanin sojojin Najeriya da na Burkina Faso domin magance kalubalen ta’addanci da tada kayar baya.
“Na zo kuma game da ta’addanci da tada kayar baya a kasashenmu domin neman shawararku da gogewar ku tunda Najeriya ta tsunduma cikin yaki da wannan annoba,” in ji shi.
(NAN)