Gwamnatin tarayya da wakilan kungiyar kwadago ta kasa (TUC) sun sake fara wani taron tattaunawa kan tabarbarewar cire tallafin man fetur.
An fara taron ne da misalin karfe 5 na yamma a fadar shugaban kasa ta Aso Rock Villa Abuja.
KU KARANTA: Za a Fara Kwashe Maniyyatan Kano A Yau Lahadi
Idan za ku iya tunawa kungiyoyin kwadagon da suka hada da kungiyar kwadago ta Najeriya NLC da TUC, sun yi wata ganawa da gwamnati a ranar Larabar da ta gabata.
A taron na yau, na gudana ne bisa jagorancin tawagar gwamnatin tarayya na karkashin sakataren gwamnatin tarayya (SGF), Sanata George Akume.
Sauran sun hada da gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele; tsohon gwamnan jihar Edo, Comrade Adams Oshiomhole; da kuma babban jami’in rukunin kamfanin mai na Nijwriya (NNPCL), Mele Kyari.
Haka kuma a cikin taron akwai sakataren zartarwa na hukumar bunkasa ciwon sukari ta kasa (NSDC), Zacch Adedeji; Mataimakin shugaban kasa na kasa, na NNPC, Yemi Adetunji; tsohon kwamishinan yada labarai da dabaru na jihar Legas, Mista Dele Alake; da Hon James Faleke, da dai sauransu.
A bangaren TUC akwai mambobi bakwai, karkashin jagorancin shugabansu, Mista Festus Osifo.
Alake ya ce bayan taron da aka yi a makon da ya gabata za a ci gaba da tattaunawa kan yadda za a magance dukkan batutuwan da ke gabansu.
A wani labarin kuma: Gwamnatin Kano Ta Gargadi Masu Farwa Kayan Al’ummah Da Sunan Ganima
Gwamnatin Jihar Kano ta yi gargadi da kakkausar murya, ga al’ummar Jihar cewar baza ta lamunci afkawa gine ginen mutane da sunan cin ganima ba.
Wannan gargadi kuwa ya haɗar da dukkan sassan jihar baki daya.