Gwamnatin Najeriya ta kulla yarjejeniya da gwamnatocin Japan da Isra’ila kan kera babura masu amfani da wutar lantarki a kasar.
Yarjejeniyar wani mataki ne na farko ga Da zai kai ta zuwa wani yanayi na musamman, yayin da kasar ke kokarin rage fitar da iskar Carbon da kuma da ake da shi wajen kawo karshen matsalar sauyin yanayi.
Jakadan Isra’ila a Najeriya, Michael Freeman ya ce, hadin gwiwar da ta hada da fasahohin Isra’ila da Japan da Najeriya za ta taimaka wajen magance dimbin kalubalen da suka shafi harkokin sufuri da muhalli a Najeriya.
KARANTA ANAN: Cikar Jihar Enugu Shekaru 31: Gwamna Ugwuanyi Ya Yabawa Iyayen Da Suka Kafata
“Aiki ne na hadin gwiwa tsakanin kamfanonin Isra’ila da Japan da Najeriya da zai gudana a Najeriya.
“Abin da ke da muhimmanci game da wannan aikin shi ne, wani shiri ne na fargar jaji, wanda ya hada fasahohin Isra’ila, fasahohin Japan, don kasuwancin Najeriya da kirkire-kirkire tare domin samar da wata kafa da zata yi aiki sosai.
Farfesa Mohammed Haruna, Mataimakin Shugaban Hukumar NASENI ya yaba da hadin gwiwar, yana mai cewa ta zo a daidai lokacin da ake fatan samun ta.
A wani labarin kuma: Ambaliyar Ruwa Ta Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane Hudu A Plateau
Akalla mutane hudu ne suka mutu sannan wasu suka jikkata sakamakon mamakon ruwan sama da aka yi a kauyukan Nyelleng da Gwabi na karamar hukumar Pankshin ta jihar Filato.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Daga cikin wadanda suka mutu akwai wasu ma’aurata da aka bayyana sunayensu da Daniel Goma da matarsa da kuma wasu mutane biyu. Shugaban karamar hukumar Audu Kak’mena ya ziyarci al’ummar yankin domin jajantawa al’ummar yankin.