Japan ta bayyana wasu Dalilai daya sanya ba zata turowa Najeriya Kayayyakin Yaƙi ba
Gwamnatin Ƙasar Japan ta bayyana dalilan da suka sanya ba zata iya sayar da ko makami guda ga Najeriya, duk da ta’addancin Boko Haram, da ƴan ta’adda, da sauran matsalolin tsaro dake fuskantar Ƙasar.
Wakilin Japan a Najeriya, Mr Kuzuyoshi Matsunaga ya bayyana haka a ranar Alhamis a Abuja, a lokacin da yake taro da Hukumar Kula da Cigaban Yankin Arewa Maso Gabas ƙarƙashin Jagorancin Shugaban ta Mr. Mohammed Alkali.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yanzu Lokacin Yarbawa ne su Mulki Najeriya — Inji Tinubu
A cewar sa, Gwamnatin ba zata turo da kayan yaƙin Soji ga Najeriya, sakamakon dokar da aka sanya na amfani dasu.
Ya bada tabbacin cewa Gwamnatin Japan zata cigaba da goyon bayan Hukumar dake yankin Arewa maso Gabas, gami da inganta ƙawancen Ƙasashen guda biyu.
“A Japan, Kafafan Yaɗa Labarun su, suna bada rahoto a Najeriya bawai akan ƙwallo ba, har da na Boko Haram a yankin Arewa Maso Gabas. Amma da yawa daga cikin Al’ummar Japan sun kasa fahimtar cewa akwai masu tsaurin addini a yankin Arewa Maso Gabas, amma a gaskiya babu.
“Babban dalilin shine yadda zamu magance Talauci, inganta tattalin arziki. Wannan shine ɓangaren daya fi kowane muhimmanci. Sun buƙaci Japan data bada goyon baya. Amma saboda taƙaitar Dokar Soja, ba zamu iya turo da kayan yaƙi na Soji ba.