Labarin da ke shigowa Jaridar Dimokuradiyya ya nuna cewa; gwamnatin jihar Neja ta sanar da biyan hukumar shirya jarabawar kammala karatun Sakandare ta NECO bashin kudi har naira miliyan 200 domin ganin an sako wa daliban jihar sakamakon jarabawar su, wanda adadin daliban ya kai mutum dubu 30.
Kakakin gwamnan jihar Neja, Mary Berje ce ta bayyana a ranar Talata a garin Minna, inda ta ce a cikin shekara uku da suka gabata, gwamnatin ta kashe kudin daya kai kimanin naira biliyan 1 wajen samar da ilimi kyauta ga daliban jihar Neja.