Daga wakilin Dimukaradiyya Mukhtar Yakubu.
An bayyana na jari Hujja a matsayin wata hanya da ta hana masana’antar fina-finai ta Kannywood ci gaba, wanda kuma hakan ne ya sa, har ta samu kan ta a matsayin da ta samu kanta a yanzu.
Daya daga cikin Dattawa a masana’antar Shehu Hassan Kano ne, ya bayyana hakan ga wakilin jaridar Dimukaradiyya a lokacin da su ke tattauna wa da sh,i dangane da yanayin da harkar fim ta ke ciki a yanzu.
Shehu Hassan Kano ya ce “Yanzu idan ka duba kungiyoyi wadanda su ya kamata su jagoranci wasu kungiyoyin su, ba wani abu gare su ba. Idan ma ka ba su Mukami sai ka ga da shi da iska duk daya ne, don mun samu kan mu a Kano kungiyoyin ba sa gudanar da aikin su yadda ya kamata” inji shi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Tsohon shugaban sojin Jihar Oyo ya rasu
Ya Kara da cewa, “Idan kuma ka yi magana, sai su ce ai “Kare da kudin sa sai ya sha rubutu”, don haka sai ai Maka yi rashin kunya. Idan ma ka ce kada ka Kara ganin su a wajen ka, a matsayin ka na Shugaba, to sai su tafi wani gari suna harkokin su. domin kasuwar ba taka ba ce kai kadai, don haka ba za ka Hana mutum ya yi kasuwancin sa ba” kamar yadda ya bayyana.
Kazalika Shehu Hassan ya ce, “To wannan ita ce matsalar da aka samu. Amma dai ba na so a ce kyara ba zai samu ba, sai dai dole sai an bi hanyar hadin kai da kuma hakuri, a nan gyara zai samu. Su manyan su zo a yi don Allah, su kuma yaran su kalli manyan a matsayin na gaba da su. ” Inji Shehu Hassan Kano.