Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta tabbatar da mutuwar wani jariri dan wata bakwai da mata hudu a wani hatsarin kwale-kwale a karamar hukumar Guri.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda a jihar, DSP Lawan Shiisu, ya tabbatar da faruwar lamarin a Dutse ranar Larabar nan.
“A ranar Talata, da misalin karfe 6 na yamma, bayanan da muka samu sun nuna cewa a ranar da misalin karfe 4:30 na yamma wasu mata hudu da wani yaro suka hau kwalekwale daga Nguru jihar Yobe zuwa kauyen Adiyani da ke karamar hukumar Guri ta jihar Jigawa.
Karanta kuma: Hatsarin Kwale-Kwale Ya Hallaka Mutum 5 A Jihar Jigawa
“Abin takaici, kwalekwalen ya kife kusa da inda suke. Direban ya yi nasarar tsira da rai, yayin da fasinjojin suka nutse a ruwan,” in ji Shiisu.
Ya ce nan take wasu mutane a yankin suka yunkuro domin ceto fasinjojin, inda ya ce sun kwaso gawarwakin.
Shiisu ya ce an kai gawarwakin zuwa asibitin Adiyani kuma likita ne ya tabbatar da cewa sun mutu.
Ya kuma bayyana sunayen matattun a matsayin Oneyaniwura Kasagama, mai shekaru 50; da Lafiya Bulama, mai shekaru 40; sai Badejaka Kasagama, mai shekaru 40; Gimto Kasagama mai shekaru 40 da Mai Madu Bulama, jariri dan wata bakwai.
Kamfanin dillacin labarai na kasa NAN ya rawaito cewa Kakakin ya ce wadanda abin ya shafa dukkansu mazauna kauyen Adiyani ne, inda ya kara da cewa an fara gudanar da bincike kan lamarin.
A wani labarin kuma: An Tsare Mai Shiga Tsakanin ‘Yan Bindiga Da Fasinjojin Jirgin Kasan Kaduna
Alhaji Tukur Mamu, jagoran masu sasantawa tsakanin ‘yan bindiga da fasinjojin da aka yi garkuwa da su daga wani jirgin kasa mai zuwa Kaduna a watan Maris, an kama shi a birnin Alkahira, babban birnin kasar Masar, tare da iyalansa.
Mamu wanda ke kan hanyarsa ta zuwa kasar Saudiyya don gudanar da aikin Hajji, an tsare shi na tsawon sa’o’i 24 a filin jirgin sama na Alkahira, kuma ana shirin dawo da shi gida Nijeriya.