Wani mummunan lamari ya faru a Kano ranar Talata yayin da wani jariri dan watanni 19 ya nutse a cikin rijiya da ke unguwar Al-Ansar da ke karamar hukumar Danbatta a jihar.
Lamarin da ya yi sanadin mutuwar jaririn, ya faru ne a lokacin da mahaifiyarsa ba ta kusa da wajen.
Da yake tabbatar wa jaridar Daily trust faruwar lamarin, Kakakin Hukumar Kashe Gobara ta Jihar, Alhaji Saminu Abdullahi, ya ce sun samu kiran gaggawa daga wani mutum Mai suna Salisu Bello inda suka aika da tawagar ceto zuwa wurin.
“Rundunar ta fitar da gawar yaron da ba ta da rai daga rijiyar yayin da Hukumar ta fara binciken lamarin,” in ji shi.
Abdullahi ya kara da cewa an mika gawar yaron ga kakansa, Malam Abdulkadir domin binne shi.
Ya kuma yi kira ga iyaye da su kula da harkar ‘ya’yansu domin gujewa irin faruwane hakan a gaba.