Daga Mukhtar Yakubu
A cikin masana’antar finafinai ta Kannywood, tsohuwar jaruma Fadila Jalal ta kasance jarumar da ta yi shuhura kuma a aka yi yayin ta a shekaru kamar 17 da suka wuce, wadda ta kasance a lokacin, kowa labarin ta ya ke.
Sai dai, bayan lokaci da ta yi aure, sai aka daina ganin ta, duk da dai auren bai dade ba ta sake dawowa harkar fim. Amma ba ta yi wani tasiri ba. Haka dai ta ci gaba da Gararamba har ta samu ta yi wani auren, wanda shi ma ba ta dade ba ta sake fitowa, amma ta yi sa’ar haihuwa guda biyu, ko da yake, daya daga ciki ya mutu yanzu sai guda ne kawai a raye.
Tun daga lokacin dai, da ta ga harkar fim ta juya mata baya sai kuma ta koma wajen ‘yan Faira ta samu Lamunin fara bege. Hakan ya sa ta koma yawon wakokin yabon Manzon Allah S A W, tana zuwa gidan biki tana yi.
A kwanakin baya na yi hira da ita take cewa da ni, “Ita babu ruwan ta da harkar fim kuma ba ta tare da su, don haka ma ba ta shiga cikin su, saboda haka babu ruwan ta da su. Ita kawai yanzu tana harkokin ta ne na yabon Manzon Allah S.A.W.” inji ta.
Cikin Kalaman nata, ta nuna harkar fim Kamar wani aikin Sabo ne, sai dai ta ce, ba za ta manta da harkar ba, saboda a dalilin ta ne, ta je aikin Hajji da umrah, amma a yanzu ba ta cikin ‘yan fim kuma babu wata harkar da ta ke hada su, kamar yadda ta bayyana.
To sai dai wani abu mai kama da almara, sati biyu da yin wannan hirar, sai muka hangi Farida Jalal a cikin’ yan fim suna aiki tare wajen Daukar wakar siyasa, tare da duk jaruman fim a Katsina,
Ko da muka tambaye ta, a kan wannan sai cewa ta yi, “Ai waka ce ba fim ba ne,” amma dai daga karshe da na matsa mata da tambaya ta ce, ko yanzu ta samu fim za ta yi daman ai don ba a saka ta ne, ya sa aka daina ganin ta. Inji Farida Jalal.
Comments 1