Masana’antar shirya fina-finai ta Bollywood dake ƙasar Indiya masana’anta ce wadda ta tara al’umma da dama, kama daga jarumai da mawaƙa da daraktoci da makiɗa da sauransu kuma maza da mata.
Daga cikinsu akwai masu shaye-shaye na giya dana sigari inda a yanzu ma har ana zargin wasu da shan miyagun ƙwayoyi a masana’antar. Sai dai akwai jaruman da a can baya sunyi sabo da shan taba sigari amma kuma duk sabon da sukayi da ita sun daina sakamakon wasu dalilai.
Ga jerin jarumai guda 7 da suka yi nasarar daina shan taba sigari:
1. Salman Khan: shidai wannan jarumi yana daga cikin jaruman da suke shan tabar a shekarun baya, amma da wata cuta ta kamashi wadda dayaje asibiti sai aka gayamasa cewar cutar da take damunsa gana da alaƙa da shan taba sigari da yakeyi. Daga jin haka shikuwa ya daina shanta kwata-kwata.
2. Ajay Devgan: Wannan jarumi ya kasance yana auren jaruma Kajol, amma lokacin da mahaifin Kajol ya rasu a asibiti shine aka tabbatar da akwai illar shan sigari a mutuwar mahaifin nata inda bayan rasuwar ne ya shiga damuwa, sannan kuma ga mijin NATA wato Ajay shima yana sha, ganin irin damuwar data shiga hakan yasa ya daina shan sigari gabaɗaya.
3. Aamir Khan: Shima wannan jarumi ya kasance yana shan sigari a shekarun baya, amma ‘ya’yansa guda biyu namiji da mace wato Junaid Khan da kuma Ira Khan sun nuna ɓacin ransu akan shan tabar dayakeyi. Bayan matarsa ta haifarmasa ɗansa na uku wato Azad tun daga nan Aamir Khan ya daina shan sigari domin kada ‘ya’yan nasa sushiga damuwa da yawa.
4. Saif Ali Khan: Wannan jarumi yayi fama da jinya sosai a asibiti inda zuciyarsa ta musa bugawa. Tun daga lokacin ya daina shan sigari sannan kuma giyar dayasaba sha itama ya daina kwata-kwata.
5. Fardeen Khan: Bayan rasuwar mahaifinsa inda da likitoci suka aunashi suka gani lallai kusan taba sigari ce tayi sanadiyyar rasuwar mahaifin nasa tun daga lokacin ya daina shan taba.
6. Jarumi Viver Ovoroi: ganin yadda yaga masu fama da ciwon daji lokacin daya je ziyara wani asibiti hakan ya sanya shi ya firgita yace ya daina. Wanda ayanzu wannan jarumi yana daga cikin masu yaƙi da shan tabar.
7. Hrithik Roshan: Wannan shahararren jarumi kusan duk rashin lafiyar da zaiyi idan yaje asibiti sai acemasa cutar tana da nasaba da shan taba sigari shikuma kwai sai ya daina, tun daga lokacin harya zuwa yanzu baisake sha ba.