Wasu daga cikin jaruman Kannywood sun Fantsama cikin siyasa, inda suka rungumi jam’iyyar ADP.
Jam’iyyar ADP itace jam’iyyar da Sha’aban Sharada ke takara gwamnan mai cike da sarkakiya a cikinta, sakamakon yadda ake taƙaddama kan tikitin takarar tsakaninsa da Koguna.
Daga cikin jaruman da suka tsaya takara a jam’iyyar sun haɗar da Adam Abdullahi Adam, da aka fi sani da Daddy Hikima ko Abale, sai Aminu Ladan Abubakar wato Alan Waƙa.
Sauran sun haɗar da Naziru Auwal da aka fi sani da Naziru Dan Hajiya, da sauran su, kuma wasu daga cikin su yan kungiyar nan ta 13X13 ce da mawaka da jarumai suka samar don ganin sun ci gaba da tallata yan takara.
Sha’aban Sharada dai tsohon mai taimakawa shugaban kasa Muhammad Buhari ne, kan kafofin yada labarai, kuma yanzu haka tuni ya bar jam’iyyar da ubangidan nasa yake wato APC, tare da komawa jam’iyyar ADC.
KARANTA ANAN: Da Dumi-Duminsa: Kwamishinan Legas Ya Yi Murabus Bayan Rushewar Ginin Oniru
Mawakin siyasar nan Dauda Rarara shima ya bar tsohon mai gidansa Abdullahi Umar Ganduje tare da komawa wajen Sha’aban.
A wani labarin kuma: Hatsarin Kwale-Kwale Ya Hallaka Mutum 5 A Jihar Jigawa
Rahotanni sun ce mutane 5 ne suka mutu yayin da aka ceto wasu hudu daga wani hatsarin kwale-kwale a karamar hukumar Gwaram da ke jihar Jigawa.
Wani mazaunin garin ya shaidawa DAILY POST cewa lamarin ya faru ne a ranar Juma’a a kauyen Martaba a lokacin da fasinjojin ke komawa gida bayan kammala sallar Juma’a.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa, DSP Lawan Shiisu Adam ya tabbatar da faruwar lamarin.