kevin hart

Jarumin Barkwanci Kevin Hart An Nemi Ya Biya Dala Miliyan 60 Kan Bidiyon Batsa

Tsohuwar Abokiyar mu’amalan dan wasan fim din kasar Amurka, Kevin Hart ta bukaci ya biya ta dala miliyan 60 a kan bidiyon batsansu tare wanda aka sake kwanakin baya.

Rahotanni sun bayyana cewa Sabbag (wacce suka yi bidiyon batsan tare da dan fim din, ta ce jarumi ya dauke ta bidiyon ne ba tare da sanninta ba a wani tafiya da suka yi zuwa garin Las Vegas a shekarar 2019 a otel din Las Vegas.

Sabbag ta ce jarumin tare da abokinsa suka shirya haduwar da suka yi da shi a garin Las Vegas in ji rahotanni daga TMZ. Ta ce a lokacin Kevin yana neman karen suna ne saboda yana da wani gala da zai yi na ban dariya, shi yasa shi da abokinsa suka boye kameran.

Jami’an tsaro sun kama abokin jarumin, Jonathan Jackson a yayin da ya ke kokarin sayar da bidiyon inda jarumi Hart ya bayyana hakan a matsayin cin zarafinsa da abokinsa ya so ya yi. Jackson, ya karyata zargin da ake masa, a yayin hukuma ta caje shi da aikata laifuka Biyu wadanda ya hada da cin zarafin Hart ta hanyar neman ya biya shi kudi idan har bai so ya fidda bidiyon.

Duk da hakan, kafafen yada labarai na TMZ ta samu wani takardar kotu wanda aka aikawa kotu a madadin Sabbag mai bukatar Hart ya biya ta kudi dala miliyan 60 a kan saka ta da ya yi cikin wannan lamari.

A karar da aka mikawa kotun an bayyana cewa jarumi Hart ya bar abokinsa, Jackson cikin dakin da suka kama a otel din Cosmopolitan saboda ya dauke su bidiyo a yayin da suke jima’i da juna

Kada ku manta jarumin bai dade da samun lafiya ba daga hatsarin motan da ya samu a cikin kwanakin baya da suka gabata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *