Duk da yadda ƙwallon ƙafa take a halin yanzu kuma ake ci gaba da zamanantar da ita duba da cewar a dukkannin wasannin da ake dasu a duniya babu wasan da ya kaita farin jini kuma a kafi rinjaya sosai da sosai, haka zaliki ita ƙwallon ƙafa a ko da yaushe fafata ta akeyi walau a wasannin rukuni na ko wacce nahiya kokuma wasannin gasar zakaru na kowacce nahiya daga cikin nahiyoyin da ake dasu a duniya.
Haka zalika koda ba’a fafata wasannin rukuni-rukuni to zakaga ana fafata gasar cin kofin duniya ko gasar cin kofin nahiyar turai ko gasar cin kofin nahiyar Afrika ko gasar Copa America kokuma gasar yankin Asia inda itadai ƙwallon ƙafa za a iya cewa a ko da yaushe ba a hutawa ana fafata ta, matuƙar aka ga an huta da fafata ta to abin yayi tsamari da yawa, ga babban misali yadda cutar Coronavirus ta gallazawa duniya yasa komai ya tsaya cik ciki harda gasar ta ƙwallon ƙafa.
Sai dai duk da ci gaba da fafata wasannin da akeyi a halin yanzu akwai manyan masu horas wa a duniya da suke a ƙasa wato basu da ƙungiya kokuma ƙasar da suke horas wa, waɗannan masu horas wa suna da yawa sosai amma kuma jaridar www.dimokuradiyya.com.ng ta zaƙulo manyan masu horas wa guda 10 da kowannensu bashi da wata ƙungiya da yake horas wa a halin yanzu kokuma babu wata ƙasa da yake horas wa.
Sai dai daga cikin masu horas war wasu korarsu akayi daga ƙungiyoyin ƙwallon ƙafan da suke horas wa, sannan wasu daga cikinsu ajiye aikinsu suka yi, haka zalika wasu daga cikinsu kuma wata gagarumar matsalarce tasa basa koyarwa yayin da wasunsu kuma za a iya cewa hutawa sukeyi kafin zuwa nan gaba su dawo horas wa gadan-gadan kenan a duniyar ta ƙwallon ƙafa kamar yadda suka saba yi a shekarun baya kenan.
Amma ita harkar horas wa ba lallai sai mai horas wa ya buga ƙwallon ƙafa ba yake yinta amma kuma mafi yawansu sun fafata wasannin ƙwallon ƙafa kafin su fara horas war inda bincike ya nuna cewar ma sune sukafi yawa a halin yanzu a duniyar ta horas da wasan na ƙwallon ƙafa.
Ga jerin masu horas war guda 10 kamar haka:
1. Massimiliano Allegri ɗan asalin ƙasar Italiya.
2. Mauricio Pochettino ɗan asalin ƙasar Argentina.
3. Ernesto Valverde ɗan asalin ƙasar Andalus.
4. Maurizio Sarri ɗan asalin ƙasar Italy.
5. Laurent Blanc ɗan asalin ƙasar Faransa.
6. Luiz Felipe Scolari ɗan asalin ƙasar Brazil.
7. Quique Setien ɗan asalin ƙasar Andalus.
8. Marcelino ɗan asalin ƙasar Andalus.
9. Luciano Spalleti ɗan asalin ƙasar Italia.
10. Leonardo Jardim ɗan asalin ƙasar Portugal.
Dukkanin masu horas war da aka lissafa sunayensu a sama to basa horas wa a halin yanzu, inda wasu daga cikinsu sun kai shekaru 4 wasu 3 wasu 2 wasu kuma 1 basa horas wa.