An bayyana jerin sunayen mutanen da suka fi kowa arziki a duniya a farkon shekarar 2023, kuma an samu gagarumin sauyi.
A cewar Forbes, Elon Musk ya rasa kambunsa na attajirin da ya fi kowa kudi a duniya ya yin da Bernard Arnault, wani hamshakin attajiri dan kasar Faransa ya doke shi.
KARANTA WANNAN LABARIN: CBN Ya Sake Fitar Da Sabbin Bayani Kan Dawo Da Tsofaffin Takardun Kudin Naira Yayin Da Wa’adi Ya Kusa
Dangote ya ci gaba da rike matsayinsa na attajirin da ya fi kowa kudi a Afirka da matsayi 34 fiye da babban abokin hamayyarsa a Afirka, Johann Rupert.
Mujallar Forbes ta fitar da jerin sunayen mutanen da suka fi kowa kudi a duniya a cikin makonni biyun farko na shekarar 2023.
Bernard Arnault, Shugaba, kuma Shugaban LVMH Moët Hennessy Louis Vuitton yanzu yana kan gaba da darajar dala biliyan 209.3.
Attajirin dan kasar Faransa ya sha gaban shugaban kamfanin Tesla, Elon Musk wanda ya kalli yadda dukiyarsa ta ragu a watannin baya zuwa dala biliyan 146.
A cikin wannan lokacin a bara shekarar 2022, Elon Musk ya yi kama da wanda ba za a iya taɓa shi ba tare da ƙimar sa kusan dala biliyan 300.
Sauran hamshakan attajirai a saman biyar har zuwa ranar Asabar 14 ga watan Janairun 2023 sun hada da Gautam Adani, attajirin dan kasar Indiya yana da arzikin da ya kai dala biliyan 128.3.
Jeff Bezos, Shugaba na Amazon ya zo na uku da dukiyar da ta kai dala biliyan 121.3 yayin da Larry Ellison, shugaban kamfanin Oracle ya kammala na biyar da darajar dala biliyan 110.4.
Warren Buffett – dala biliyan 110.4bn
Bill Gates – dala biliyan 103.7bn
Carlos Slim Helu & dangi- dala biliyan 89.8bn Mukesh
Ambani – dala bliyan 88.4bn
Francoise Bettencourt Meyers & family – dala biliyan 81bn
Dangote ya kasance mutumin da ya fi kowa kudi a Afirka
Aliko Dangote ya ci gaba da rike mukaminsa na attajirin da ya fi kowa kudi a Afirka inda ya mallaki dala biliyan 13.5 a ranar Asabar, 14 ga Janairu, 2023.
Sai dai Dangote bai sake shiga cikin jerin attajirai 100 ba, inda ya kasance na 134 a jerin masu kudi a duniya, a cewar Forbes.
A matsayi na biyu a Afirka shi ne Johann Rupert daga Afirka ta Kudu wanda ke da dala biliyan 10.7 a sunansa. Nicky
Oppenheimer – dala biliyan 8.5bn
Abdulsamad Rabiu- dala biliyan 7.3bn
Nassef Sawiris- dala biliyan 7.3bn
Mata 25 mafi arziki a 2023, 10 sun fi Dangote arziki
A wani labarin kuma, jerin sunayen matan da suka fi kowa kudi a duniya a shekarar 2022.
Yawancin sunayen 25 sun kasance a saman teburin jerin masu arzikin mata tsawon shekaru yanzu.
Duk da haka, akwai babban canji a cikin jerin yayin da tsohuwar mace mafi arziki a duniya ta ragu zuwa matsayi na 8.
A wani labarin kuma, Yadda Budurwa Yar Yiwa Kasa Hidima Ke Sarrafa Kwallo Kamar Pele, Maza Sun Jinjina Mata
Wata budurwa mamba a hukumar yi wa kasa hidima NYSC a halin yanzu ta fara jan hankula saboda kwarewarta ta wasan kwallon kafa.
Budurwar ta yi kyau sosai, da ta dauko kwallon ta yi wasa da ita, sai ga maza suka tsaya sekeke suna binta da kallon salon yadda take lelaya kwallo.
So I love market
I Love market and I am Happy to going market and I love business
I love business and I am doing to business and I like it and I am Happy to doing business.