Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona ƙungiya ce wadda tunda ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Bayern Munich ta gigita ta a gasar zakarun nahiyar turai daci 8 da 2 ta shiga neman ‘yan wasa domin yin garambawul da cikakken gyara na kaucewa irin kwatankwacin abin daya faru domin gudun maimaici.
Hakance ta sanya suka sallami wasu tsofaffin ‘yan wasan ƙungiyar ƙwallon ƙafan da ake ganin cewar shekarunsu yaja sosai da aka ganin cewar sune matsala a ƙungiyar ƙwallon ƙafan ta Barcelona da suka haɗar da Ivan Rakitic da Aturo Vidal da kuma Luis Suarez da sauransu inda dukkaninsu an sallamesu basa tare da Barcelona a halin yanzu.
Garambawul ɗin dai ba iya kan ‘yan wasa ya tsaya ba harda mai horas wa inda suka sallami Quique Satien suka maye gurbinsa da tsohon ɗan wasansu wato Roland Koeman ɗan asalin ƙasar Netherland, haka zalika a halin yanzu ana ta shirye-shiryen yaya za a yi shugaban ƙungiyar ƙwallon ƙafan ta Barcelona ya sauka duba da yadda ake ganin shima yana da matsala.
Tun kakar wasan data gabata Barcelona tayi yunƙurin dawowa da Neymar amma abin yaci tura sosai, haka zalika a kakar wasa ta bana Barcelona ta nemi ‘yan wasa da dama domin yin garambawul amma kuma ‘yan kaɗan suka iya saye daga cikinsu, sai dai daga cikin waɗanda ba a sami nasarar sayensu ba kuma gashi har an rufe hada-hadar kasuwar sayen ‘yan wasa amma kuma Barcelona ta bayyana cewar zata koma nemansu domin a sayarmata dasu a watan Janairu na sabuwar shekarar 2021 idan ta kama inda ake ganin za a sake buɗe hada-hadar kasuwar sayen ‘yan wasan.
Ga jerin sunayen ‘yan wasan da Barcelona ta nema amma batasami damar sayensu ba:
Akwai Menphis Depay na Lyon da García da Lotaro Martínez na Inter Milan da Neymar na PSG da Wijnaldum na Liverpool da Mohammed Salah shima daga Liverpool da Barnado Silva na Manchester City da Alaba na Bayern Munich da Jadon Sancho na Brussia Dortmund da Richarlison na Everton da Olmo da Gómez da Gayà da Torres da Angeliño da Estupiñán da Bernat da Aït-Nouri da Stengs da Sarr da Sessegnon da kuma Guendouzi.