Ƙwallon ƙafa tana daga cikin wasannin da suka fi shahara a dukkanin wasannin da ake dasu a duniya kuma kusan a yanzu itace ta farko a wasan da yafi kowanne farin jini duba da yadda akeyinta ako wacce nahiya daga cikin nahiyoyin da ake dasu a duniya.
Sannan Faransa ta yi manyan ‘yan wasa da dama a tarihinta da suka buwayi duniya a duniyar ƙwallon ƙafa, ita kanta a harkar ƙwallon ƙafa ana yiwa ƙasar ta Faransa laƙabi da The Blues.
Awajen ‘yan wasan da sukafi yawan jefa ƙwallaye ga ƙasar ta Faransa wato wajen ajiye tarihi kenan jaridar Dimokuraɗiyya ta zaƙulo jerin ‘yan wasan da suka fi yawan jefa ƙwallye.
Ga jerin sunayen ‘yan wasan kamar haka:
1. Thierry Henry ya jefa ƙwallaye 51.
2. Michel Platini ya jefa ƙwallaye 41.
3. Oliver Giroud ya jefa ƙwallaye guda 40.
4. David Trezeguet ya jefa ƙwallaye 34.
5. Zinedine Yazid Zidane ya jefa ƙwallaye 31.
6. Antoine Griezmann ya jefa ƙwallaye 31.
Daga cikin jerin ‘yan wasan guda 6 da aka lissafa guda 4 sun rataye takalmansu inda har yanzu Oliver Giroud da Griezmann suna buga wasa, shin ko a cikinsu akwai wanda zai karya tarihin da Thierry Henry ya kafa? Lokaci ne dai zai nuna idan har hakan zata kasance.